ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (I)

by Umar Shuaibu and Mairo Muhammad Mudi
6 months ago
Suleja

Kalilan ne daga cikin mutane suke da masaniyar cewa, garin da ake kira Suleja a yau, shi ake kira da Abuja kafin shekarar 1979, wato shekaru 45 da suka gabata.

Daya daga cikin tsofaffin Ministocin Babban Birnin Tarayya (FCT), kuma mashahurin marubucin zube, marigayi Janar Mamman Jiya Vatsa, ya taba rubuta waka a shekarar 1982; inda ya ce, “Abuja garina ce, amma kasa ta bukace ta. Na ajiye ta, na kuma ba kasa suna. Suleja ita ce garina yanzu, Abuja kuma garinmu gaba-daya. Na taba mallakar Abuja, amma yanzu ita ce ke da ni.”

  • Kasafin Kudi Na Naira Tiriliyan 1.78 Na Abuja Ya Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
  • Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya

Da a ce Janar Vatsa yana raye a yau, da watakila zai kara wasu kalmomi ya ce; “Na taba mallakar Abuja, amma yanzu Abuja ta mallake ni, kuma ta hana ni walwala.”

ADVERTISEMENT

Dangane da matsayinta a taswirar kasa, Suleja tana tsakanin layuka biyu madaidaita, wadanda ke siffanta kusurwa a saman taswirar FCT, abin da ke nunawa a fili cewa; an ware ta da gangan daga FCT kafin kaddamar da aikin kwamitin Aguda. A bayyane yake cewa a farko, an shirya amsar dukkan masarautar Abuja baki-daya ne.

Marigayi Farfesa Akin Mabogunje, a cikin jawabinsa yayin bikin cika shekaru 30 da kirkiro Abuja, ya bayyana cewa; shi da kwararrun masana kimiyya 12 da ya jagoranta, sun zauna a Suleja tsakanin shekarun 1976 da 1978 domin gudanar da bincike kan muhallin kasa da kidayar asalin mazauna yankin.

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

A wancan lokacin, Sarkin Abuja shi ne Marigayi Sulemanu Barau, wanda ya rasu a shekarar 1979. Saboda hikimarsa da hangen nesa, ya ga cewa zai fi dacewa mutanensa su samu ‘yanci da asali ta hanyar kasancewa cikin wata jiha a kasar tarayya, fiye da su kasance a cikin wani yanki da ake kira kasar kowa ba tasa ba, kamar yadda ake kallon FCT a yanzu.

A sakamakon haka, kashi 80 cikin dari na kasar da ke karkashin Masarautar Abuja da sunanta gaba-daya, aka mika wa gwamnatin tarayya domin gina FCT. Wannan kaso ya yi daidai da 80 cikin dari na jimillar fadin FCT a yanzu. Sauran kashi 20 cikin dari kuwa, an samo su ne daga tsohuwar Jihar Filato da tsohuwar Jihar Kwara, wato Nasarawa da Kogi a halin yanzu.

Daga baya kuma, an sauya sunan garin zuwa Suleja a shekarar 1979, a girmama Marigayi Sulemanu Barau. sauran kasar 20 cikin dari yanzu su ne suka zama Kananan Hukumomin Suleja, Gurara da Tafa a Jihar Neja.

A karshe dai, yau dukkanin asalin mutanen Masarautar Suleja kafin kirkiro FCT, wato wadanda ke wajen FCT; amma cikin Jihar Neja da kuma ‘yan’uwansu daga kabilun Gbagyi, Koro da wasu da ke cikin FCT, sun zama tamkar marasa tushe ko makoma, suna kallon zuwan FCT a matsayin masifa maimakon albarka. Asalin mazauna FCT, na fafatawa da sauran ‘yan Nijeriya wajen mallakar kasa, wadanda ke da karfi na kudi da tasiri fiye da su.

‘Yan Nijeriya na da fa’ida biyu, zai iya zama dan asalin jiharsa kuma ya nemi mukami ko kujerar siyasa a nan da kuma FCT. Amma dan asalin FCT, ba zai iya samun irin wannan dama a wasu jihohi ba, saboda za a dauke shi a matsayin bako.

Haka kuma, dukkanin mutanen Jihar Neja da ma sauran ‘yan Nijeriya na gasa da mutanen Suleja wajen mallakar kasa a Suleja, saboda kusancinta da babban birnin tarayya, muddin suna da karfin kudi da goyon bayan gwamnati daga Minna. Duk da haka, ta halin da ake ciki da dabi’ar mutane, kowa ya fi jin dadin zama a kasarsa fiye da kasar da ba tasa ba.

Asalin mazauna Abuja ko da suna cikin Suleja ko FCT, sun takaita ne kawai a yankunansu, suna cikin gasa mai tsauri da sauran ‘yan Nijeriya. Hanyarsu mafi rinjaye ta samun abinci, ita ce noma, amma mallakar gonaki da gidaje a kauyukansu yanzu ya zama tarihi. Yawancin matasa ba su da karfin saye, sai dai su kama haya a garuruwansu, domin zama da iyalinsu; abin da yawancin al’umma ke kallo tamkar sabo da al’ada. Abin da ake tsoro da yake faruwa a FCT yanzu, ya fara bayyana har ma a makwabciyarta, Suleja.

Halin da suka ci gaba da shiga ya karu ne sakamakon jahilci da kin neman ilimi daga wasu, wadanda ke yada karya ga jama’a. Wani tsohon dan jarida ya rubuta a jaridar Sunday Tribune ta 28 ga Janairu 2024 cewa, gwamnatin tarayya ta biya diyyar asalin mazauna FCT, kuma ta gina musu Suleja. Wannan na nufin cewa; har ma tsofaffin ‘yan jarida da dattawan kasa suna da fahimta maras tushe cewa, Suleja ginin gwamnatin tarayya ne bayan kirkiro FCT.

Tambayoyin da suka dace a yi su ne; ko an biya Suleja diyya ne dangane da kafa FCT? Ko kuwa ana ba mazaunanta kulawa daidai da sauran al’ummomin Jihar Neja, wajen samar da ababen more rayuwa da ayyuka? Idan FCT na da fa’idodi, wa ke amfana da su, Suleja ko jihar?

Za mu ci gaba a mako mai zuwa 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja
Manyan Labarai

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su
Manyan Labarai

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Next Post
An Ziyarci Gidajen Tarihin Kasar Sin Sau Biliyan 1.49 A Shekarar 2024

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.