Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago ya bayyana cewa sulhu da ‘yan bindiga da wasu jihohin makwabta suka yi ne ya janyo kwararowar su zuwa cikin jihar.
Yayin da yake yin Allah-wadai da kutsen da barayin shanu da ‘yan bindiga ke yi a jihar, Gwamna Bago ya ce, shi ba zai yi wani Sulhu da ‘yan bindiga ba.
- An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara
- An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan aiwatar da dokar tabbatar da tsaro da duba lafiyar dabbobi ta jiha da aka gudanar a Minna babban birnin jihar.
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba.
Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp