Super Falcons sun dawo kasar bayan ficewarsu daga gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA 2023 da ke gudana a Australia da New Zealand.
An fitar da tawagar Randy Waldrum daga gasar bayan da Ingila ta doke su da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a ranar Litinin.
- Sin Ta Yi Tir Da Umarnin Amurka Kan Sake Bitar Batun Zuba Jari A Kasashen Waje
- Gwamnatin Sojin Nijar Ta Yi Sabbin Nade-Nade
Wasu yan tawagar da suka hada da Asisat Oshoala, Rasheedat Ajibade, Osinachi, Chiamaka Nnadozie, Gift Monday da Rofiat Imuran sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a daren Laraba.
Bayan isowarsu filin jirgin saman, shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya,Alh Gusau, shugaban hukumar kwallon kafa ta Legas, Fouad Oki, da wasu manyan mutane ne suka tarbe su.
Za a iya tunawa cewa babban kocin kungiyar, Randy Waldrum, ya bar Australia sa’o’i kadan bayan ficewar kungiyar daga gasar cin kofin duniya.
Rahotanni sun ce Waldrum ya bar sansanin tare da yan wasa na kasashen waje.
Yan wasan da suka tafi tare da kocin mai shekaru 66 zuwa Amurka sun hada da Michelle Alozie, Jennifer Echegini, Esther Okoronkwo, Ifeoma Onumonu, Deborah Abiodun da Toni Payne.