Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Super Falcons ta Nijeriya, waɗanda suka lashe gasar WAFCON sau 10, sun iso Abuja bayan nasarar da suka samu a gasar cin Kofin Mata ta Afirka (WAFCON) ta shekarar 2024 a Morocco.
Kungiyar ta samu wannan nasara ne bayan ta doke Morocco da ci 3-2 a wasan ƙarshe da aka buga a Rabat ranar Asabar.
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Nuna Wa Afrika Ta Kudu Kwanji A Pretoria
- WAFCON 2025: Yau Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Moroko A Wasan Ƙarshe
’Yan wasa da jami’ai da sauran mambobin tawagar sun sauka a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 2:25 na rana a ranar Litinin.
Bayan isowarsu, tawagar na shirin gudanar da taron murnar nasara ɗauke da kofin tun daga kan titin filin jirgin saman Abuja zuwa Fadar Shugaban Ƙasa, inda ake sa ran za a karɓe su tare da girmamawa daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Super Falcons sun kafa tarihi na samun nasarar WAFCON karo na 10 a ranar Asabar, bayan da suka doke Morocco saboda irin ƙwazo da jajircewar da suka nuna a fili.