Wata mata sabon aure ta babbake mijinta ita kuma ta kashe kanta har lahira saboda zarginsa yana cin amanar ta.
Matar mai suna Ife, ta kashe mijin nata mai suna Bolu saboda zarginsa da cewa wai yana ha’intarta a bayan idonta.
Hakan yasa ta yanke irin wannan Danyan Hukuncin bayan ta shaida aikata hakan a shafin sada zumunta na manhajar WhatsApp, tace “Sakamakon kaita bango da yayi, to yau kafin faduwar rana za’a fasa kukan duka su biyun”.
Mijinta Marigayi Bolu, yana zaune ne a Cairo, amma ya kan ziyararci Nijeriya, ta kone shi ne a cikin gidansa, inda ta hada da shi da dukiyar sa.
Bayan Ife din ta gudu ne sai aka ruga da Bolu zuwa asibiti. Rahotanni sun nuna cewa, daga baya an gano gawar Ife din, wacce ake zargin ita ce ta kashe kanta.
Shima Bolu, daga baya yace ga garin ku nan, a sakamakon kunan da ya mamaye mafi yawan sassan jikin sa. Inji rahoton shafin Labarun Hausa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp