Hukumar kwallon kafa da ke shirya babbar gasar Laliga ta kasar Sifaniya ta dauki matakin cire sunan sabon dan wasan Fc Barcelona, Dani Olmo sakamakon kasa yi mashi rajista da kungiyar ta yi.
Da yammacin yau Laraba, kwararren dan jaridar kasa da kasa akan harkar wasanni Fabrizio Romano ya bayyana cewar, an cire sunan Olmo daga jadawalin yan wasan Barcelona da suka cancanci buga gasar Laliga.
Barcelona na ta kokarin ganin ta yi wa Dani Olmo wanda yazo daga kungiyar kwallon kafa ta RB Leibzig a bazara rajista,hakan yasa ta garzaya kotu har sau biyu amma hakar ta ba ta cimma ruwa ba a dukkan kararrakin da ta shigar.