Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da tsaftar yara mata wadanda suka fara tasawa. Sau da dama za a ga kananan yara masu tasowa, na zama da kazantar jiki, ko tufafi, ko kuma wani waje da aka ware musu daban kamar daki, ta yadda za a ga yarinya tamkar wadda ba ta da masu fada mata ta ji. Wanda hakan ke sawa da yawan mutane idan sun ci karo da irin yaran marasa tsafta, kazamai za su fara zagin iyayen yaran a cikin zuciyarsu, tare da yin alkalancin ba wa yarinya rashin gaskiya, ko kuma uwar yarinyar. Duk da cewa iyayen yara na iyakar kokarinsu wajen ganin sun koyar da su tsaftar da ta dace, sai dai su ma yaran ba kyalle ba ne dungu ne, musamman wajen yin watsi da dukkanin abin da iyayen ke nuna musu. Yayin da wasu iyayen kuma ba sa nuna halin ko in kula ga yaran nasu wajen koyar da su tsafta, tamkar dai ba su suka haifa ba. Ko laifin waye tsakanin iyayen da yaran, Me ya ke janyo haka kuma ta wacce hanya za a magance matsalar? Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa, inda suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Sunana Haleema Khabir (Nana Haleema) Jihar Kano:
Wannan tun daga gida abin yake farawa, sai sun ga na gaba da su ya gyara sannan su ma za su yi nasu kokarin dan su gyara, in na gaba ba su gyara ba babu bakin da za a tsawatarwa na kasa ya gyara. Rashin kula ne da rashin sanin mahimmacin ita kanta tsaftar daga wajan iyayenmu mata da ‘yan uwanmu mata manya da muke zaune gida daya da su. iyaye mata da kuma ‘yan uwa mata wanda suka fi na kasa shekaru. Kamar yadda na ce in uwa ba ta gyara ba ta bar kanta kaca-kaca yaro yana tasowa yana ganinta a haka da abin da zai tashi kenan shi ma, ice tun yana danye ake tankwara shi, wani lokacin irin wadannan iyayen za ki ga ko kwalliya suka yi a gida za ki ji yara suna Mama unguwa za ki? Sabida ba a saba ganin hakan ba. Yara suna ganin haka ba za su mayar da hankali wajan gyara ba sai ki ga duka gidan an taru an zama abu guda. Ta hanyar nutsuwa da mayar da hankali ba fada ko tsawa ba, da wasa da dariya uwa za ta koyawa ‘yar ta abubuwa da dama wanda har abada ba za ta manta ba. sai sun gyara sannan su ma za su gyara, wani lokacin iyayen suna da tasu tsaftar yaran ne babu to ba zuba musu ido a matsayinki na uwa ya kamata ki yi ba, ko da kanki ki saka ‘yar ki a bandaki ki wanke ta ai ke kika haife ta yi mata hakan da za ki yi shi ne zai saka ko baki sakata ba za ta yi da kanta, musamman wacce ta fara girma sosai da zarar an mata haka shikkenan an kamo lagonta ba za ta sake bari hakan ta faru ba.
Sunana Rabi’atu Abdullahi Aminu (Ouummey), daga Jihar Kano:
A gaskiya wannan matsala tana samo tushe ne daga iyaye mata, a bisa al’ada uwa mace ke da alhakin tsaftar ‘ya’yanta, wannan wani koyarwa ne da yake farawa tun daga shekarun yarinta wato 5 zuwa sama, sai dai dama an ce daga na gaba akan gane zurfin ruwa, wato wasu iyayen su kan su basa kula da tsaftar kan su balle ‘ya’yansu masu tasowa su yi koyi, a wasu lokutan kuma za ki ga san jiki da lalaci ke saka iyaye sakar wa yara ragamar kula da rayuwar su, daga lokacin da yarinya ko yaro ya kai ya iya wanka da tsarki da kansa za ki ga an kyale shi da kan sa, ba za a yi masa ba sai dai a jira yayi da kansa, wannan zai sa ka ga yara kamar ba ‘ya’yan mutane ba wasu. Wasu kuma laifin daga wajen marika ne, a irin ‘case’ din uwa ba ta tare da uban da sai ka ga babu wani kulawa dan matar uba na kyashin ta gyara da ko ‘yar da ba nata ba, su kuma iyaye maza ba sa sa ido kan hakan, wannan sune manyan dalilai. Laifin a mafi yawancin lokaci na iyaye mata ne, a wasu lokutan kuwa laifin iyaye maza da ba za su wadata iyalansu da kayan gyara ba kamar sabulan wanka, omon wanki da dai sauransu. ita mace uwa ce, wannan ya:sa in ta gyaru al’umma da yawa sun gyaru akasin haka ma al’umma da yawa sun cutu. A bisa dacewa tun yarinya na karama a kalla shekara biyar ya kamata uwa ta fara training dinta wajen tsafta, wanka, wanki, yankan farce, gyaran kai da sauransu. A lokacin da ‘ya mace ta fara balaga kuwa ya kamata uwa ta ware wani lokaci domin zaman karantar da ita amfanin tsafta, yadda za ta gyara jikinta da yadda za ta tsaftace muhallinta, cikin nasiha da tattausan lafazi cike da Lugga da salon magana irin na harshen uwa, ba wai cikin fada ko da zagi ba. So da yawa ‘ya’ya na koyi da ayyukan iyayensu ne dan haka ita ma uwar ya kamata ta dau matakin tsafta tukuru domin ‘ya’yanta su dauki kyakkyawan misali daga gare ta. shawara ga iyaye mata masu sakaci shi ne; su gyara wajen kula da tsaftar ‘ya’yansu domin a duk yadda yaran nan suke yana bayyana yadda iyayen suke ne, ma’ana yanayin yaran na bayyana yanayin tsaftar iyaye, muna fata za su kiyaye kuma a gyara domin rage matsaltsalun lafiya da kuma aurarrakii. Ouummey.
Sunana Fadimatuz Zakiyya M Dahir (Zee MD) daga Jihar Kano:
Gaskiya rashin tsaftar ‘Ya’ya mata daga cikin gida take samo asali, da yawa iyaye mata ba sa kula da yaransu a lokacin da suke farkon balaga, da zarar sun ga yarinya ta iya wanka da kanta sai a sakar mata ragamar komai, Kuma daga wannan lokacin uwa ba za ta dunga saka ido ta ga yaya yarinyar ta ta take gudanar da tsaftar jikin nata ba. A gaskiya a wannan bangaren iyaye mata suna da laifi sosai. Laifin iyaye ne, sune suke janyo hakan da kansu, akwai iyaye mata da yawa wadanda basu damu da gyara jikinsu ba balle kuma su kula da tsaftar yaransu, hakan na janyo yarinya ta tashi da rashin gyara da tsafta. Hanya daya ce ya kama iyaye Mata su bi wajen koyar da yaransu tsafta. Yana da kyau ace tun tasowar yaranki su budi ido da ganin Mahaifiyar su tsaf, ya kasance koda yaushe kina cikin tsafta da gyara gidanki da su kansu yaran, hakan yana sawa yaro ya taso cikin koyi da hakan. Duk abin da ya kasance kazanta ne yana da kyau uwa ta nisance shi, to inda yara suka taso suka ga hakan a tare da Mahaifiyar su sukan yi koyi su ma. Shawara ta ga iyaye Mata shi ne; Su kasance masu kula da tsaftar yaransu, kar ki bar yarinyar ki don ta fara komai da kanta ki saka Mata idanu, yana da kyau koda yaushe ki kasance cikin buncikar yadda take tsaftar jikinta tun daga kan wanka, yanken farce, da gyaran gashin kanta, tare da kula da duk wata kusurwa ta jikinta, idan har ki ka kasance kina kula da tsaftar jikin yaranki to tabbas koda ba kya tare da su za su kasance masu dorewa da hakan, domin dama kin horesu akan hakan, don Allah iyaye mata mu kula da tsaftar jikinmu tare da yaranmu, don koda baki koyar da yaranki tsafta ba in har kin kasance me tsafta to za su taso cikin koyi da ke. Bissalam
Sunana Aysha Adam Alhassan Dan Fulani (Fulani):
A gaskiya a nawa bangaren laifin na iyaye ne duba da cewa idan har mutum ya taso ya ga ana yi to tabbas babu abin da zai hana shi yi, ba iya kan irin wadanan ‘ya’yan ba, hatta da gidajen da suka fito za ki ga su ma ba damuwa sukai da gyaran ba banlanta idan anga mutum buzagadi a nusasheshi don gyarawa. Hanyoyin gyarawa shi ne; dole sai uwa ta zama jajirtattaciya wurin tsaftace kanta, sannan ‘ya’yanta za su yi koyi da ita, wasu yaran ba sai kin ce musu wance je ki yi wanka ba wallahi da kansu za ki ji suna mama ni dai wanka zan yi. So irin wannan abubuwan na samo asali daga wurin iyaye ne, ubangiji ya ba mu ikon gyarawa. Don Allah mata mu mike mu tsaya tsayin daka domin mu ga yaranmu sun fito tsaf-tsaf! wallahi akwai wadanda na sani idan har basu gyara yaransu ba a makaranta idan sun je dasu babu masu daukar musu, wasu ko saboda yadda suke dagewa suke gyara abunsu za ki ga har rige-rige ake wurin daukar su. Na gode.
Sunana Safiyya Mukhtar Garba daga Jihar Kano Sharada Phase 3 Ja’en Yamma Layin Shago Tara:
Wannan abin dama tun tuni ya riga ya zama ruwan dare gama duniya, kuma ba kowa ke da laifi ba fa ce iyayen yara, barin uwa, domin kaso kusan saba’in na alhakin tarbiyyantarwa ya rataya ne a wuyanta yayin da a kalla kashi talatin yake kan uba, kuma yawanci idan aka ga haka yara ba sa kokarin tsafta to daga iyayensu ne domin dana gaba ake ganin zurfin ruwa, iyaye su za su yi kokari su gyara sannan su samu bakin tsawatarwa da ‘ya’yansu. Laifin Iyaye ne, rashin sanin ka’idojin addini da rashin sanin darajar kai, wani lokaci kuma tsantsar talauci yana kawo hakan. Da farko sai ita kanta uwa ta gyara sannan za ta iya fadawa ‘yar ta ta ji, sannan sai sun cire kunya tsakaninsu da ‘ya’yansu sannan za su iya zagewa su koya musu sannan ta hanyar saurarar wa’azi da fadakarwa na malamai mata da ake yi. Shawara ita ce su dage su kuma daure su dinga cire kyashi da ganda suna koyar da ‘ya’yansu tsafta domin nan gaba gidajen mazajensu za a kai su, ba su ce sun girma ba za su yi musu ba daga haka suke lalacewa.
Sunana Nazifi Ahmad Chikawa daga Chikawa Karamar Hukumar Madobi Jihar Kano:
Ita tsaftar jiki da tufafi tana nufin kawar da dukkan wani datti daga jiki ko tufafi ta hanyar amfani da ruwa, sabulu da sauransu.Tun asali iyaye ke sakin ragamar kula da tsaftar yaransu a hannun yaran, wanda hakan kuskure ne, domin daga lokacin da yarinya ta fara girma a lokacin ya kamata a nuna mata muhimmancin kula da tsaftar jikinta. Uwa ita ce babbar mai laifi, saboda uwa ita ce mai kula da dukkan tarbiyyar yaranta fiye da uba, kuma tsafta tana daga cikon addini domin “Allah mai tsarki ne, kuma ba ya karbar komai sai mai tsarki”. Ba kowacce uwa ce take jawo yarinyarta a jiki ta nuna mata yadda za ta tsaftace kanta da tufafinta ba a yanzu, saboda duhun kai ko kuma kunya, wanda hakan ba ya cikin tsarin addinin musulunci. Hanya ta farko shi ne; iyaye mata su rika jawo yaransu mata a jika su mayar da su tamkar kawayensu kuma abokan shawararsu. Hakan zai saka yara mata bayyana dukkan wata matsala ko damuwarsu ga iyayensu musamman abin da ya shafi jikinsu. Su kuma iyaye mata za su samu damar koyawa yaransu hanyoyin da za su tsaftace jikinsu cikin sauki cikin hikima. Tun ran gini tun ran zane, duk yadda yarinyarki ta ga kin taso cikin kazanta da rashin tsaftace jikinki ko cikin tsafta da kula ita ma a haka za ta taso. Don haka a matsayinki na uwa ya kamata ki kasance mai tsaftace jikinki da tufafinki da gidanki a koda yaushe. Hakan zai sanya duk abin da kika fadawa yarinyarki akan tsafta ta dauke shi da gaske kuma da muhimmanci, domin Barewa ba ta gudu danta kuma ya yi rarrafe. Sannan uba shi dole ya kasance mai kula da tsaftar matarsa da yaransu duk lokacin da yake a gida.
Sunana Muhammad Murtada (Bazazzagin Mai Iyali) Zaria City:
Tabbas! so da yawa ni kaina na kan ji ba dadi idan na ga yadda wasu ‘ya’ya matan ke tafiyar da rayuwar su ba a cikin tsari ba musamman ta fannin rashin sanin yadda za su tsaftace jikkunansu. A gaskiya game da rashin sanin yadda yara za su tsaftace jikinsu zan iya ba da laifi kaso tamanin 80% cikin dari akan iyaye mata, wanda kuma kaso ashirin 20% kan iya kasance wa laifin iyaye maza. Uwa ita ce makaranta na farko akan ‘ya’yanta wanda kuma Uba yake biye mata, a matsayinta na Uwa ta fi Uba sanin mene ne matsalar ‘yar ta mace da kuma wani lokaci ya kamata ace tayi wannan ko ta bar wancan. Shawarata ga iyaye mata ya kamata ace su maida hankali akan ‘ya’yansu mata musamman ta fannin tsaftace jikkunansu, kuma ba dai-dai bane ki ce sai ‘yar ki ta girma sannan za tasan me ya kamata tayi na tsaftace jikinta domin hakan kuskure ne babba. Kuma shi ma Uba ya kamata ya rika ba da na shi gudummuwar ta hanyar ba da duk wani Abun buÆ™ata domin tsaftace jikkunansu.
Sunana Hannatu Mahmud Birnin Yeron Jihar Kaduna a tarayyar Nijeriya:
Tun farkon fari wannan abu yake wato daga gida domin iyaye mata da suke zaune a gida yadda suka tafiyar a haka za a tafi, idan basu nuna ko kuma ba a ga suna yi ba to taya yarinya za ta taso ita ma tayi, haka zalika idan kannenta suka taso haka za su tafi su ma domin hausawa na cewa daga na gaba ake gane zurfin ruwa, kuma inda akuyar gaba ta sha ruwa na baya ma idan ta zo anan za ta sha. Laifin iyaye mata ne sau tari kuma da wasu mazan, idan aka ce mace to ita ce kan gida duk wata tsafta ta jiki ko ta muhalli (gida) wajen iyaye mata ya kamata ya taso tunda sune suke rayuwa ko yaushe a ciki. Wasu mazan kuma kamar yadda na anbata sukan gaza wajen wadata iyalinsu da abubuwan da ya kamata ayi tsaftar kamar irinsu Sabulu, Omo da sauransu. A har kullum mace ita ce gida kuma uwa saboda a duk lokacin da mace ta zamo babu tsafta tabbas gida ya lalace. Hanyar daya kamata iyaye su bi shi ne; yarinya dai gabanki ta taso tun farkon fari kenan sanya ido gareta wajibi ana nuna mata yadda za ta tsaftace jikinta da duk abin da ya kamata ta tsaftace ta hanyar nutsuwa da laluma bada tsawa ko fada ba. Shawara ita ce ya kamata iyaye su kasance sun sanya idanu akan ‘ya’yansu, su nuna musu muhimmancin tsafta a rayuwarsu dama addininsu baki daya, yo idan ma yarinya taki tana ganin kanku daya tsaf ki dam keta ki sata ban daki ki sutaleta idan ta ga hakan za ta hankalta. Allah ya sa mu dace.
Sunana Safna Sani Jibiya (Mumyn Ihsan), Jihar Katsina, Karamar Hukumar Jibiya:
Gaskiya hakan ba daidai ba ne, yarinya mace tun tana karama ya kamata ace ana tsaftace mata jikinta wanda hakan zai sa ta tashi da hakan ya zame mata jiki, yayin da koya mata sauran ababen tsaftace jiki za su zo mata cikin sauki ba tare da an sha wahala ba, kasantuwar ta saba da hakan tun tana karama. Laifin uwa ne uwa tana taka muhimmiyar rawa wajen koya wa yarinyarta mace tsafta, tarbiyya, iya magana, kwalliya da iya shiga ta kamala da sauransu, saboda ita ce take zame maki abokiyar shawara a gaba, yarinyarki duk abin da ta tashi ta ga kina yi to tabbas za ta koya saboda haka ke kanki ya kamata ki iya wadannan abubuwan domin samawa yarinyarki ingantacciyar rayuwa. Idan kinajin nauyin koyawa yarinyarki wani abu musamman yadda za ta tsaftace kanta ki koya ki jata a jikinki kina yin abu tana taya ki tun tana karama, yi kaza daina kaza, miko mun wancen, ajiye wancen, gyara wancen, ba wai cikin tsawa da hantara ko kyarar ta ba hakan zai sa ta saba kuma ta koya cikin sauki. Ki kasance mai sakarwa yarinyarki fuska ko yaya ne ba a ce kullum kina a murtuke ba gaskiya, wannan shi ne. Wannan ai babban sakaci ne muke yi, A gaskiya kar mu yadda ma yarinya ta kai 7-8 bata san ya za ta iya tsaftar jiki ko muhalli ba, kina nuna mata ta hanyar wanke inners da sauran lunguna na jiki saka kamshi da sauransu, ya kamata muna kiyayewa gaskiya, saboda in har za ki ce sai gaba to tabbas Ina gaya maki wannan gaban nan cizon yatsa za kina yi wallahi. Saboda ta saba abin da ta saba tun farko ba za ta daina ba, saboda haka mu kiyaye. Safna Sani Jibiya.