Mahukuntan kasar Sin sun fitar da wani rahoto game da yadda aka tafiyar da tattalin arzikin kasar a watan Nuwamban bana, a ranar 16 ga wannan wata, a daidai wannan lokaci kuma, ra’ayoyin jama’a na kasa da kasa sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana farfadowa sannu a hankali, lamarin da ya tabbatar da abun da aka bayyana yayin taron tattaunawa kan aikin kula da tattalin arzikin kasar na kwamitin kolin JKS da aka kammala ba da dadewa ba.
An lura cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da samun bunkasa yadda ya kamata tun daga watan Satumba, sakamakon kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha. Kana karuwar sayayyar kayayyaki ta taka rawar gani ga ci gaban tattalin arzikin kasar. A cikin muhimman ayyuka guda tara da aka tsara a taron tattaunawa kan aikin kula da tattalin arziki na kwamitin kolin JKS, akwai batun fifita bukatun gida su kasance a matsayin koli. Dalilin da ya sa haka shi ne domin tattalin arzikin kasar yana da tushe mai karko, da fifiko masu yawa, da juriya mai karfi, da kuma babban karfin samun bunkasa a boye. Kuma, gwamnatin kasar ta fitar da wasu manufofin da suka dace, duk wadannan za su taimakawa ci gaban tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.
Hakazalika, huldar diflomasiyya dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya tana aza harsashi mai kyau ga cudanyar tattalin arziki dake tsakaninta da sauran kasashe. Kana kokarin da kasar Sin take yi wajen habaka ginin shawarar ziri daya da hanya daya, da zurfafa tsarin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen mambobin BRICS, shi ma yana kara karfafa huldar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da sauran kasashen. (Mai fassara: Jamila)