Shugaba Bola Tinubu ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na kawo karshen ta’addanci da kuma dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a fadin Nijeriya.
Shugaban ya tabbatar da cewa, Gwamnatin Tarayya tana hadin gwiwa da wasu kasashen duniya don karfafa tsaron kasa da kuma kawar da duk wata barazana ga zaman lafiyar kasar.
- An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato
- Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025
Da yake jawabi a lokacin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, Tinubu ya ce, duk da kalubalen tsaro da tattalin arziki da ake fuskanta a yanzu, gwamnatinsa ta ci gaba da mai da hankali kan Ajandar Sabunta Fata ta gina kasa mai arziki da tsaro.
“Duk da matsalolin siyasa da muke fuskanta, mun ci gaba da hadin gwiwa da abokan huldarmu ta hanyar diflomasiyya.
“Ina tabbatar muku da cewa, ta’addanci ba zai yi nasara ba. Aikin da ke gabanmu shi ne, mu ci gaba da ajandar Sabunta Fata don gina Nijeriya mai arziki da wadata,” in ji Tinubu.














