A gun taron manema labaru da ma’aikatar tsaron kasar Sin ta gudanar a kwanakin baya, kakakin ma’aikatar ya yi bayani game da rahoton ‘yancin zirga-zirga a teku na shekarar 2023 da ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta gabatar cewa, ‘yancin zirga-zirga a teku ba ya nufin yin zirga-zirga ba bisa ka’ida ba. A cikin rahoton, Amurka ta zargi kasashe da yankuna 17 ciki har da kasar Sin da batutuwa 29 game da cin moriyar teku fiye da kima.
A shekarun baya-bayan nan, Amurka ta yi amfani ‘yancin zirga-zirga a teku don nuna karfin sojanta da yin atisayen soja na hadin gwiwa a teku. Tun daga shekarar bara zuwa yanzu, kasar Philippines ta shiga yankin tudun ruwa na Ren’aijiao da tsibirin Huangyan na kasar Sin sau da dama, kana Amurka da Japan da Philippines sun gudanar da taron koli na bangarorin uku kan batun yankin tekun kudancin Sin. A matsayin bangaren da ya sa kaimi ga tada rikicin, Amurka sau da dama ta yi amfani da ‘yancin zirga-zirga a teku.
- Tsarin Kiwon Lafiyar Yaran Kasar Sin Na Kara Kyautata, In Ji Jami’ar Hukumar Lafiyar Kasar
- Sin Da Kasashen Larabawa Za Su Gaggauta Aikin Kafa Al’umma Mai Makomar Bai Daya
Bangaren Amurka na da wata ma’anar ta daban game da “yancin zirga-zirga a teku dake cikin yarjejeniyar dokar teku ta MDD. A cikin yarjejeniyar MDD, an ba da wannan ra’ayi don tabbatar da kasa da kasa su samu moriyar teku da odar teku a duniya. Amma a bangaren Amurka, tana son tabbatar da muradunta ta fuskar diplomasiyya da aikin soja da kuma danniya a teku.
Amurka ba ta sa hannu kan yarjejeniyar dokar teku ta MDD ba, amma ta yi amfani da ‘yancin zirga-zirga a teku don zargin wasu kasashe game da moriyar teku, yunkurinta shi ne kiyaye danniya a teku na duniya. (Zainab Zhang)