Assalamu alaikum. Akramakallahu barka da warhaka tambaya gareni.
mutum ne zai je umara cikin azumi sai ya zama jirginsu zai tashi karfe biyu na ranar, shin zai kame baki ne daga safe zuwa lokacin tashin ko kuwa ba zai yi azumi ba kwata-kwata a ranar?
Wa alaikum assalam, Zancen mafi yawan malaman Hanafiyya da Malikiyya da Shafi’iyya shi ne : idan mutum ya yi tafiya a tsakiyar yini, to ba zai ci abinci ba, saidai idan ya shiga wahalar da ba zai iya jurewa ba, amma a wajan malaman Hanabila ya halatta, saboda Allah ya halattawa matafiyi cin abinci a suratul Bakara kuma bai bambanta tsakanin wanda ya yi tafiya a farkon yini ba, da wanda ya yi a tsakiya. Don neman karin bayani duba : Al’insaf 3/205 Allah ne mafi sani.
**********************************************
Na Ci Abinci Bayan Alfijir Ya Keto, Yaya Hukuncina?
Malam jiya bayan na gama cin abinci, sai na samu ashe alfijir ya keto, tun kafin na fara ci, saidai Allah ya sani, na ci ne a rashin sani, ko ya zan yi yanzu ? Amsa: To malam mutukar ba da saninka ka yi haka ba, to azuminka ya inganta, domin duk lokacin da mai azumi ya yi kokwanton hudowar alfijir, to ya halatta a gare shi ya ci abinci, saboda wanzuwar dare shi ne asali, kamar yadda Ibnu-abbas yake cewa : “Allah ya halatta mana cin abinci – a Ramadhana- mutukar mun yi kokwanton hudowar alfijir”, saidai in da zai yi kokwanton faduwar rana to bai halatta a gare shi ya ci abinci ba, saboda wanzuwar ranar shi ne asali.
Allah ne mafi sani.