A yau Asabar, bayanai a hukumance sun nuna cewa, fiye da fasinjoji tsakanin yankuna miliyan 304 ne suka yi zirga-zirga a fadin kasar Sin a ranar Juma’a, rana ta hudu ta hutun bikin bazarar bana, yayin da aka samu yawan ziyarce-ziyarcen iyalai wanda ya ingiza yawon shakatawa.
Wannan dai shi ne karo na farko na zirga-zirgar bikin bazara na bana, wanda kuma aka fi sani da chunyun, da adadin tafiye-tafiye tsakanin yankuna ya zarce miliyan 300, a cewar wata tawagar ma’aikata ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirga a lokacin chunyun.
Adadin tafiye-tafiye ta mota ya karu da kashi 6.9 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda ya kai miliyan 288.44 a ranar Juma’a, yayin da tafiye-tafiye ta jirgin kasa da ta jirgin sama ya karu da kashi 5.3 cikin dari da kashi 3.6, bi da bi. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)