• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Takunkumai Kan Kamfanonin Sin Ba Su Ne Maganin Rikicin Ukraine Ba

byCGTN Hausa
2 years ago
Sin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana matukar adawa da haramtattun takunkumai daga bangare guda da Amurka ta kakkabawa kamfanonin kasar. Haka kuma ta bayyana cewa, kasar za ta dauki matakan da suka wajaba, don kare halastattun hakkokinta, da moriyar kamfanoninta yadda ya kamata. 

Abu ne da ya zama wajibi, kowace kasa mai cikakken iko, kuma wadda ta san ciwon kanta, ta tabbatar da kare moriyarta da na al’ummomi da dukkan wani abu mallakinta. Haka kuma, dole ne a rika tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, wato kamar yadda Sin ta bayyana cewa za ta dauki matakan da suka wajaba na kare muradunta.

  • Adadin Kamfanonin Waje Dake Zuba Jari A Sin Na Karuwa
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Fara Farfadowa Mai Karfi A Wannan Shekara Wanda Ya Sa Duniya Amincewa Da Shi

Sai dai, bisa wani yanayi mara dadi da daukacin duniya ke ciki, da kira da burin da kasashen duniya ke da shi na ganin kyautatuwar mu’amala tsakanin manyan kasashen biyu, wato Sin da Amurka, kiran da ake yi har kullum shi ne, a kai zuciya nesa, a girmama tare inganta tattaunawa da juna. Bai kamata Amurka ta rika takala har ta kai Sin ga mayar da martani ba.

Dakile alaka ko kamfanonin Sin ko kuma katse huldar Sin da Rasha, ba shi ne zai kawo karshen rikicin Ukraine ba. Sin mai kaunar zaman lafiya, ta sha bayar da shawarwarin yadda za a shawo kan rikicin, haka kuma tana ci gaba da yin iyakar kokarin ganin an tsagaita bude wuta, sai dai da alama, tamkar ana tufka ne da warwara, domin yayin da take neman shawo kan rikicin, har yanzu wasu kasashen yamma na ta matsa kaimi wajen goyon bayan wani bangare tare da tallafa masa, lamarin da kowa ya san cewa, ba hanya ce ta samar da maslaha ba.

Zuwa yanzu bisa la’akari da halin da duniya ta shiga, ya kamata mu gane cewa, takunkumai ko fito na fito ko karfin soji, ba za su kawo karshen rikicin ba, ganin yadda aka shafe shekaru 2 ana gwabza fada amma babu alamar tsagaituwarta. Yanzu lokaci ne da ya kamata a sauya dabara, domin lalubo mafita mai dorewa ga rikicin, ba tare da sanya siyasa ko bata alaka ko dora laifi kan wata kasa ba. (Fa’iza Mustapha)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Mun Hana Kai Wa ‘Yan Bindiga Burodi Ba Hana Sayarwa Ko Gasawa Ba – Dauda

Gwamnatin Zamfara Za Ta Gina Tashar Motocin Tilera Biyu A Birnin Gusau

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version