Wani masani kan harkokin tsaro, Christopher Oji, ya alakanta yawaitar ayyukan zamba (yahoo) ta yanar gizo da aikata manyan laifuffuka a Nijeriya kan talauci da rashin aikin yi.
Oji ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ranar Talata a Legas.
- Yahoo-yahoo: Mutum 6 Sun Shiga Hannun ‘Yansanda Bayan Barkewar Rikici Kan Raba Dala 3,800
- EFCC Ta Ƙi Amincewa Da Barin Godwin Emefiele Tafiya Neman Lafiya Ƙasar Waje
NAN ta bayyana cewa, ma’anar zamba (yahoo) ta yanar gizo ita ce, aikata laifuka ta hanyar kwamfuta da intanet don sace kudin mutane.
Oji, wanda tsohon shugaba ne a kungiyar ‘yan jaridu ta kasa bangaren masu rahoto labaran ta’addanci da aikata laifuka (CRAN), ya bayyana cewa, aikata laifuka ta yanar gizo babbar barazana ce ga tsaro da tattalin arziki ga al’ummar kasa, ya kuma bukaci gwamnati ta dauki matakin gaggawa.
A cewarsa, yawan talauci da rashin aikin yi ya sanya matasa da dama shiga ayyukan ta’addanci ta yanar gizo a matsayin hanyar gujewa wahalhalun da suke ciki na zamantakewa da tattalin arziki.