Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12.
Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce karkashin wannan tallafi, iyalai da yaransu za su ci gajiyarsa za su samu ragin kashe kudaden makaranta da yawansu ya kai kusan yuan biliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.8. (Saminu Alhassan)