Masu amfani da wutar lantarki za su biya tarar da bata yi kasa da Naira 100,000 ba, idan suka yi magudi ko kuma suka yi amfani da mitar lantarki ta haramtacciyar hanya, in ji Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya, NERC.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sabuwar doka da aka yi wa kwaskwarima kan amfani da mitar wutar lantarki ba bisa ka’ida ba wacce aka fitar a ranar Talata.
Tarar tsakanin N100,000 zuwa N300,000, ya danganta da tsarin layin wutar lantarki da mitar ke kai.