• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihi Zai Dorawa Japan Alhakin Sakin Gurbataccen Ruwan Nukiliya Zuwa Teku

by CMG Hausa
2 years ago
Japan

Da misalin karfe 1 na ranar Alhamis din nan ne, bisa agogon wurin, gwamnatin kasar Japan ta fara sakin gurbataccen ruwan tashar nukiliyar Fukushima a cikin teku wanda al’ummomin duniya masu dimbin yawa suka nuna adawa da matakin. Wannan rana ta zama ranar bala’i ga yanayin tekun duniya. Kuma gwamnatin kasar Japan ta zama mai lalata muhallin halittu da ma gurbata tekun duniya.

Shi ne karo na farko da aka saki gurbataccen ruwan nukiliya zuwa cikin teku da gangan, bayan bil’adama sun yi amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya. Masana sun yi hasashe cewa, ya zuwa yanzu, kasar Japan tana da gurbataccen ruwan nukiliya kusan ton miliyan 1.3, kuma da alamun za a shafe shekaru 30 zuwa 50 ana sakinsu zuwa teku. Bayanai na nuna cewa, watakila gurbataccen ruwan nukiliya zai mamaye kusan duk fadin tekun Pasifik.

  • Dole ne Japan Ta Dakatar Da Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku Da Bin Wata Hanya Mafi Dacewa

Sanin kowa ne cewa, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Japan ta zabi shirin sakin gurbataccen ruwan nukiliya zuwa teku a cikin shirye-shriye guda biyar, shi ne tana ganin wannan shiri ba zai lakume kudi da yawa ba kuma yana da sauki wajen aiwatar da shi.

Kasar Japan ta gamu da hadari, amma ta kawo wa duniya baki daya wannan hadari, wanda ya sanya kasa da kasa cikin tashin hankali. Firaministan kasar Japan Fumio Kishida ya sanar da cewa, zai dauki alhakin shirin sakin gurbataccen ruwan nukiliya zuwa teku. Amma a gaskiya, ta yaya ‘yan siyasar kasar Japan za su iya “daukar alhakin” wannan “hadarin” wanda ya kasance kamar wani harin da aka kai wa duk duniya, amma ba shi da shirin share fage, kuma babu hanyar rage asararsa? Kuma me za su fadawa zuriyoyinsu?

Tarihi zai dorawa Japan alhakin sakin gurbataccen ruwan nukiliya zuwa teku. (Safiyah Ma)

LABARAI MASU NASABA

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin
Daga Birnin Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Next Post
Hatsarin Kwale-kwale Ya Hallaka Rayukan Mutum 12 A Nasarawa, Majalisa Ta Jajanta

Hatsarin Kwale-kwale Ya Hallaka Rayukan Mutum 12 A Nasarawa, Majalisa Ta Jajanta

LABARAI MASU NASABA

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.