Katsina tana da tarihi mai yawa musamman na masarautun da suka yi mulkin Katsina tun farko ya zuwa yanzu, ga dai yadda Masarautun su ke.
Gidan Sarauta na Durbawa
Gidan Sarautar Durbawa shi ne asalin wadanda suka fara Sarautar Katsina. Ance an samu sunan Katsina ne bayan da wata ‘yar Sarki daga Daura wadda ta auri Janzama wanda shine Sarkin Durbawa,da ya yi mulki daga Durbi-Takusheyi wanda kuma har yanzu sunan shi an aje shi kamar dutse kusa da Mani.Babu dai wani bayanin da aka rubuta dangane da wadanda suka yi Sarauta a karkashn Masarautar.Amma Janzama shi ne wanda ya yi mulki na karshe a karkashin daular Durbawa. Kumayau ne wanda ya raba shi da mulki shi ne Sarki na farko a daular Kumayau.
Gidan Daular Kumayau
Wannan ita ce daula ta biyu bayan daular Durbawa,ta samar da Sarakunan bakwai daga Kumayau zuwa Sanau.Ita wannan daular ana nada Sarki ne ta hanyar yin kokawa inda wand ya yi nasara shi ne ake zaba sabon Sarki.
Gidan Daular Korau
Daular Korau ta samar da Srakunan Katsina 31 wanda aka fara daga Muhammadu Korau wanda shi ne Sarki na farko da yake musulmi a karkashin daula ta uku bayan ya samu nasara akan Sanau,tun daga wancan lokacin sai maganar Sarauta kuma ta koma ta gado aka barta ga sai wadanda suka gaji Sarauta.
Gidan Daular Dallazawa
An samu wannan daular ne a sanadiyar Jihadin Shehu Usman Danfodio a shekarar 1804.Jihadin ne a karkashin Malam Ummarun Dallaje,Malam Mammam Na Alhaji Malam Ummarun Dunyawa wadanda suka amshi tuta daga Malam Muhammadu Bello dan Shehu Usman Danfodiyo a madadin shi.Daular ta samar da Srakunan Katsina takwas daga Malam Ummarun Dallaje (1807)zuwa Malam Yaro a shekarar 1906.
Gidan Daular Sullubawa
Ita ce daula ta hudu bayan daular Durbawa,bayan da aka tunbuke Sarki Abubakar da Malam Yero wanda Turawan mulkin mallaka suka yi wannan shi ya bada dama ta mulkin Sullubawa ko kuma ace daular Dikko.Wannan daula ta samar da Sarakuna hudu daga Sarkin Katsina Muhammadu Dikko a shekarar 1906 zuwa Sarkin Katsina Abdulmuminu Kabir Usman Sarki na yanzu.
Sarakunan Habe
Gidan Durdawa
1.Sarkin Katsina Kumayau 2.Sarkin Katsina Rumba Rumba 3.Sarkin Katsina Bataretare 4.Sarkin Katsina Jin Marata
5.Sarkin Katsina Yankatsari 6. Sarkin Katsina Jibda Yaki (Sanau)
Gidan Korau
7.Muhammadu Korau 1348 – 1398
8.Usman Maje 1398 – 1405 (9). Ibrahim Soro 1405 – 1408(10) Marubuci 1408 – 1426
11.Muhammadu Turare 1426 – 1436
12.Ali Murabus 1436 – 1462(13) Ali Karya 1462 – 1475(14) Usman Tsaga Rana 1475 – 1525
15.Usman Damisa Gudu 1525 – 1531
16. Ibrahim Maje 1531 – 1599
17. Malam
18. Yusufu 1599 – 1613
19. Abdulkadir 1613 – 1615
20.Ashafa 1615 – 1615(21) Gabdo 1615 – 1625
22.Muhammadu Wari 1625 – 1637.
23.Muhammadu Tsaga Rana 1637 – 1649
24.Mai Daraye 1649 – 1660
25. Sulaiman 1660 – 1673
26. Usman Tsaga Rana 1673 – 1692
27.Toyariru 1692 – 1705
28. Yanka Tsari
29. Uban Yara I 1705 – 1708
30. Uban Yara II 1708 – 1740
31. Jan Hazo (Dan Uban Yara) 1740 – 1751
32. Tsaga Rana 1751 – 1764
33.Muhammadu Kayiba 1764 – 1771
34. Karya Giwa 1771 – 1788
35. Giwa Agwaragi 1788 – 1802
36. Gozo 1802 – 1804
37.Bawa Dan Giwa 1804 – 1805
38. Muhammadu Maremawa 1805 – 1806
39.Magajin Haladu 1806 – 1807
Sarakunan Fulani
Dallazawa:
40.Umarun Dallaje 1807 – 1835
41. Muhammadu Bello 1835 – 1844
42.Saddiƙu 1344 – 1869 Ahmadu Rufa’i
43. 1869 – 1869
44). Ibrahim 1869 – 1882
45.Musa 1882 – 1887
46. Abubakar 1887 – 1905
47. Yero 1905 – 1906
Sullubawa
48.Muhammadu Dikko 1906 – 1944
49.Usman Nagogo 1944 – 1981
50.Muhammad Kabir Usman 1981-2008
51.Abdulmumini Kabir Usman 2008 zuwa yanzu