Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin jam’iyya da na kasa sun ajiye kwandunan furanni don tunawa da jaruman da suka kwanta dama a filin Tian’anmen dake birnin Beijing a safiyar ranar Litinin, gabanin bikin cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin.
Wakilai daga sassa daban daban sun hadu da shugabannin don gudanar da bikin ranar shahidan kasar Sin. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)