A yau Juma’a aka kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Boao. Cikin kwanaki 4, kimanin wakilai 2,000 daga kasashe da yankuna sama da 60 ne suka hallara a lardin Hainan na kasar Sin tare da musayar ra’ayi mai zurfi karkashin jigon na “Gina makomar asiya a duniya mai sauyawa.”
A matsayinta na mai masaukin bakin, kasar Sin ta gabatar da shawarwari 4 da suka yi daidai da ra’ayin mahalarta taron. Shawarwarin sun hada da karfafa hadin kai da hadin gwiwa wajen inganta aminci, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa da dunkulewa, da samar da ci gaba da wadata na moriyar juna, da kiyaye zaman lafiya da tsaro da zaman jituwa.
Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2024, an kafa kusan sabbin kamfanoni 60,000 masu jarin waje a kasar Sin, adadin da ya karu kan na 2023 da kaso 9.9. Haka kuma, cikin shekaru 5 da suka gabata, ribar jarin kai tsaye da aka zuba a kasar Sin ta kai kimanin kaso 9, inda adadin ya shiga cikin wadanda ke kan gaba a duniya. A yayin da ake fama da rashin tabbas a duniya, kasar Sin na kara fadada bude kofarta da ingiza kwanciyar hankali a duniya mai hargitsi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp