Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi karin haske game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta a Kazakhstan, yana mai cewa, Sin na da yakininta hanyar taro, ita da sauran kasashen yankin tsakiyar Asiya biyar, za su zurfafa dunkulewa, da amincewa da juna, da gina matsaya guda ta fuskar hadin gwiwa, da zurfafa daidaiton dabarun ci gaba, da daga matsayin hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da kara kuzarin gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya.
Bisa gayyatar da shugaban jamhuriyar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, tsakanin ranekun 16 zuwa 18 ga watan nan na Yuni. (Saminu Alhassan)