Ra’ayoyi daga sassan kasa da kasa sun karkata ga muhimmancin taron kolin ASEAN-Sin-GCC karo na farko da ya gudana a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia a jiya Talata 27 ga watan nan.
Daga mahanga ta shiyya, taron bangarorin uku ya mayar da hankali ga manyan sassa uku, wadanda suka hada da gabashin Asiya, da kudu maso gabashin Asiya da yankin Middle East, tare da cewa ba kasafai ake samun irin wannan hadin gwiwar shiyyoyi a yankin Asiya ba.
A gabar da ake fuskantar tarin kalubale a matakin kasa da kasa masu matukar sarkakiya, da raunin bunkasar tattalin arzikin duniya, Sin da ASEAN da GCC na aiki tare domin gina da’irar tattalin arziki ta bai daya da ci gaba tare. Hakan ba kawai zai amfani tattalin arzikin sassan ba ne, har ma zai ingiza yanayin zaman lafiya, da ci gaba a Asiya da ma sauran sassan duniya baki daya.
Sin da kasashe mambobin ASEAN, da na GCC dukkanin su suna da muhimmanci cikin jerin kasashe masu tasowa. Wannan taron koli na hadakar sassa uku ya mayar da hankali ga zakulo sabon tsarin hadin gwiwar shiyyoyi tsakanin kasashe masu tasowa, wanda hakan ke da matukar muhimmanci. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp