Tsohon Mataimakin Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, ya yi karin haske a kan abubuwan da zai yi fashin baki a kansu a wajen taron LEADERSHIP na mako mai zuwa, wanda za a gabatar a ranar Talata a matsayinsa na mai jawabi na musamman.
Har ila yau, tsohon mataimakin shugaban babban bankin, wanda ya rikide ya koma dan siyasa ya bayyana cewa, shi da sauran wadanda za su tofa albarkacin bakinsu a wajen taron, za su warware zare har abawa a kan al’amarin da ya shafi tabarbarewar tattalin arzikin wannan kasa da kuma wahalhalun da al’umma ke fama da su tare da mayar da hankali a kan zakulo hanyoyin magance matsalolin, musamman ganin yadda matsalar ke barazanar mamaye tattalin arzikin Afirka baki-daya.
- Wa’adin Da Gwamna Kano Ya Dauka Na Yi Wa Kwamishinoni Hisabi Ya Cika: Kila Wasu Za Su Karbi Littafinsu A Hannun Hagu
- Likitocin Saudiyya Sun Yi Nasarar Raba ‘Yan Biyun Da Aka Haifa Manne Da Juna A Kano
“A nawa ra’ayin, bai kamata mu dauki wadannan matsaloli da wasa ba, domin kuwa mutane na cikin halin kunci da yunwa; don haka mece ce mafita? Ina so kowa ya yi nasa tunanin a kan wannan kafin ranar da za a gudanar da wannan babban taro”, a cewar ta Moghalu.
Sannan, ya yi alkawarin yin tambayoyi a kan wannan matsala ta tabarbarewar tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu tare da sanin hanyoyin da za a yi amfani da su wajen magance su.
“Haka zalika, akwai tambayoyi da dama da za su biyo baya a kan yadda za a warware wadannan matsaloli na tattalin arzikin kasa. Don haka, ya zama wajibi mu nemo amsoshinsu. Sannan, dole ne mu lalubo hanyoyin da za a samu mafita, amma ba ta hanyar ‘yan dabaru ba.
“Har wa yau, zan yi bayani a kan hanyoyin da ya kamata a bi, don fitar da Nijeriya daga wannan mummunan hali na tabarbarewar tattalin arziki; wanda ta samu kanta a ciki tare da hanyoyin da ya kamata a kirkiro, domin sama wa matasa ayyukan yi da kuma sake samun hanyoyin shigowar kudi da bunkasa tattalin arzikin ‘yan kasa baki-daya”, in ji shi.