Kwanan baya, an gudanar da taron masanan kasashen rukunin “Global South” a nan birnin Beijing, rukunin“Global South” wato kasashe masu tasowa da masu samun saurin bunkasuwa.
’Yan siyasa da wakilan gwamnatoci daga kasashe 76 da masana da wakilan manema labarai da dai sauransu sun halarci taron ta kafar bidiyo ko a zahiri, kasashen rukunin Global South 40 sun ba da hadaddiyar shawarar mai taken “Hadin gwiwar masanan kasashen rukunin Global South don kafa kyakkyawar makomar bil Adam mai wadata a duniya ta bai daya”, lamarin da ya samu karbuwa matuka daga kasashe masu tasowa.
- Fashewar Tankar Man Fetur A Jigawa: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Haura 180
- Rundunar Soji Ta Ƙaryata Jita-jitar Mutuwar COAS Lagbaja.
Babban sakataren ofishin shugaban kasar Comoros, kana wakili mai kula da harkokin tsaro na fadar shugaban kasar Youssoufa Mohamed Ali da shugabar kwamitin sadarwa na kasar Burundi madam Esperance Ndayizeye sun kai ga matsaya daya cewa, kamata ya yi kasashe masu tasowa da saurin bunkasuwa sun yi kokarin zurfafa tsarin hadin gwiwa tsakaninsu da kuma yin kirkire-kirkire, ta yadda za a yi iyakacin kokarin raya karfin gwadagon kai, kuma inganta mu’ammala da cudanya tsakanin wadannan kasashe na da ma’ana matuka, tattaunawa tsakanin kungiyoyin masana na taka rawar gani a wannan bangare.
Darektan sashin kula da tsara shirye-shirye na gidan talibijin na kasar Kongon Brazzaville Fefe Ngakiegni ya yi nuni da cewa, dole ne kasashe masu tasowa su hada kai, don kyautata halin da suke ciki ta hanyar hadin gwiwa da kasar Sin a mabambantan bangarorin. (Amina Xu)