Kwanakin nan, wakilan hukumomin tsaro na kasashe da yankuna fiye da 40 sun isa kasar Singapore don halarci taron tattaunawar Shangri-la da aka kaddamar da shi a yau Jumma’a.
A yammacin yau, mamban majalisar gudanarwar Sin kuma ministan tsaron kasar, Li Shangfu, ya yi hira da ministan tsaron kasar Singapore Huang Yonghong.
Bayan hirarsu, an kira taron manema labaru, inda maganar Mista Li ta ja hankalin kafofin watsa labaru na kasashe daban daban, inda ya ce, yankin Asiya da Pasific tamkar wani gidan bai daya ne na al’ummun kasashen dake yankin, saboda haka, dole ne a yi kokarin tabbatar da samun wadatuwa da kwanciyar hankali a yankin, domin wannan shi ne burin bai daya na jama’ar mabambantan kasashen dake cikin yankin. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp