• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taruka 2 Na Kasar Sin: A Kara Fahimtar Cikakken Tsarin Demokuradiyya Da Ake Damawa Da Jama’a

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Yanzu haka ana gudanar da taruku 2 wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, tarukan da suka taimakawa kasashen duniya kara fahimtar cikakken tsarin demokuradiyya da ake damawa da jama’a a kasar Sin.

Yadda aka shimfida demokuradiyya a kasa, ya dogara da yadda jama’ar kasar suka tafiyar da harkokinsu da kansu. Akwai mutane fiye da biliyan 1.4 a nan kasar Sin, adadin da ya kai kusan kashi 1 cikin kashi 5 na jimillar yawan mutanen duniya. To ta yaya mutane masu yawan haka za su bayyana ra’ayoyinsu yadda ya kamata? Ta yaya za su cimma daidaito? Ta yaya za a aiwatar da ra’ayi daya da suka cimma? Kasar Sin ta lalubo bakin zaren daidaita batutuwan, wato cikakken tsarin demokuradiyya da ake damawa da jama’a.

Wannan tsarin na demokuradiyya ya shafi matakan yin zaben, shawarwari, tsai da kuduri, kula da harkoki da sa ido, ta yadda za a saurari ra’ayoyin jama’a da bayyana burikansu a harkokin siyasar kasar Sin da ma zamantakewar al’ummar kasar, lamarin da aka ayyana shi a matsayin tsarin “demokuradiyya mafi shafar kowa, da amfani, kuma ba tare da rufa-rufa ba”.

Demokuradiyya, ba kayan ado ba ne, abu ne da ake amfani da shi domin warware matsalolin da ke addabar jama’a. Ba a raba raya al’umma mai matsakaiciyar wadata ta kowacce fuska, samun gaggarumar nasara wajen dakile da kandagarkin annobar cutar COVID-19, rika zamanintar da kasar Sin da sauran nasarorin da kasar Sin ta samu ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki, daga cikakken tsarin demokuradiyya da ake damawa da jama’a ba. Rahotanni daga shahararrun hukumomin jin ra’ayoyin jama’a na kasa da kasa sun nuna cewa, gamsuwar da jama’ar Sin suka nuna wa gwamnatinsu ya wuce kaso 90 a shekaru baya-bayan nan, lamarin da ya shaida cewa, demokuradiyya irin na kasar Sin na da kuzari sosai. (Tasallah Yuan)

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Next Post
Zaben Gwamnoni: Kotu Ta Bai Wa INEC Umarnin Amfani Da Katin Zabe Na Wucin Gadi

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin

November 8, 2025
Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.