• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tashar Chancay: Sabon Mafari Ne Ga “Tsohuwar Hanyar Inca A Sabon Zamani”

by CGTN Hausa and Sulaiman
11 months ago
Chancay

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude tashar jiragen ruwa ta Chancay ta kasar Peru, ta kafar bidiyo, tare da takwararsa ta Peru, Dina Boluarte, a fadar shugabacin kasar Peru dake Lima, hedkwatar kasar, a ranar 14 ga wata, bisa agogon wurin. Shugabannin kasashen biyu sun halarci bikin bude tashar, kuma wannan shi ne babban sakamako da aka cimma yayin da shugaba Xi ya kai ziyarar aiki a Peru, sannan kuma yana nuna kyakkyawar alaka ta dogon lokaci tsakanin al’ummun kasashen biyu. “Daga Chancay zuwa Shanghai”, ya riga ya zama wani karin magana dake samun karbuwa, wanda ya nuna fatan jama’a game da wannan sabuwar hanyar ta kan-tudu da ta teku, wadanda suka hada shiyyoyin Asiya da Latin Amurka da kasashen Caribbean a cikin sabon zamanin da muke ciki.

Wannan kuma ya shaida ra’ayin bangarorin Sin da Peru game da sabon yanayi na karuwar tattalin arzikin kasa da kasa, da kuma niyyar bangaren Peru ta shiga babbar kasuwar Sin. Tashar Chancay ba kawai sabon mafari ne ga “tsohuwar hanyar Inca a sabon zamani” ba, har ta kasance wani sabon babi ne na rayuwar al’ummar Latin Amurka da Caribbean mai dadi. A yayin ziyarar aiki ta shugaba Xi, shugabannin kasashen Sin da Peru sun rattaba hannu kan wasu muhimman takardu na hadin gwiwa, kamar shirin hadin gwiwar gina Ziri Daya da Hanya Daya, da takardar inganta yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci. Bangarorin biyu sun fitar da sanarwa ta hadin gwiwa a kan tsara shirye-shiryen zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare tsare. Daga bude tashar Chancay zuwa inganta yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci, da ci gaba da inganta tattaunawa da hadin gwiwa a fannonin ilimi, al’adu, yawon bude ido da dai sauransu, zuwa mutunta ra’ayin bangarori daban daban, da ba da shawarar yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, dukkansu sakamako ne da ziyarar aiki ta shugaba Xi ta samu, wacce ta zurfafa alaka mai dogon tarihi da ke tsakanin Sin da Peru, kana ta kara fadada sararin yin hadin gwiwa ta cin moriyar juna, ta kuma ba da sabuwar ma’ana ga dangantakar bangarorin biyu a sabon zamani, sannan ta kara sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Latin Amurka da Caribbean, da tabbatar da bunkasar kasashe masu tasowa na duniya.(Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi

Rikicin PDP: A Daina Maganar Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A 2027, A Maida Hankali Kan Jam’iyya –Saraki

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.