Kasar Sin ta hada tashar samar da lantarki mai amfani da hasken rana da karfin igiyar ruwa, irinta ta farko, da turakar lantarki.
Tashar lantarkin ta lardin Zhejiang dake gabashin kasar, wata sabuwar nasara ce wajen amfani da albarkatun makamashin ruwa da samar da sabon tsarin amfani da makamashi.
A cewar kamfanin samar da makamashi na kasar Sin wato China Energy, tashar mai mazauni a garin Wugen na birnin Wenling, na da karfin megawatt 100.
Idan aka kwatanta da tashar samar da lantarki daga makamashin kwal, sabuwar tashar na da karfin samar da lantarki da ya zarce kilowatt miliyan 100 a duk shekara, wanda zai biya bukatun gidaje kimanin 30,000 na birnin. Kana lantarkin da tashar za ta samar, zai maye gurbin ton 31,000 na kwal, tare da rage fitar da iskar Carbon Dioxide da kusan ton 85,000 a kowacce shekara. (Fa’iza Mustapha)