Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya bayyana a yau Talata cewa, tashar samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa daga injunan famfo mafi grima a duniya dake zaune a Fengning dake lardin Habei a arewacin kasar Sin ta fara aiki.
Wannan tasha ce ke amfani da injuna na famfo wajen adana ruwa lokacin da aka samar da isashen wutar lantarki, da kuma amfani da su lokacin da ake bukata. Yawan janareto masu samar da wutar lantarki da aka harhada a tashar ya kai KW miliyan 3.6, yawan wutar lantarki da za ta samar a kowace shekara zai wuce kilowatt-hour biliyan 6.6. Za a yi tsimin kwal a kowace shekara da yawansa ya kai ton dubu 480.8. Bayan an kaddamar da wannan tasha, yawan hayaki mai dumama yanayi wato Carbon dioxide da aka rage fitarwa ya kai ton miliyan 1.2, matakin da ya taka rawar gani wajen ingiza kyautatuwar tsarin makamashi da rage fitar da hayaki mai dumama yanayi. (Amina Xu)