Tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da daidaita da samun karsashi a watanni 6 na karshen shekarar nan ta 2023, bayan wanzuwar farfadowarsa a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuni.
Da yake bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Juma’ar nan, shugaban hukumar bunkasa ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar Sin Yuan Da, ya ce shaidu sun tabbatar da kyakkyawan sauyi da aka samu a alkaluman auna ci gaban tattalin arzikin Sin tun daga watan Yuli da ya gabata, ciki har da saurin bunkasar fannin samar da makamashi, da kyautatuwar fatan da ake yiwa kasuwanni, da karuwar ma’aunin alkaluman sayayya na masana’antun kasar cikin watanni 2 a jere.
Yuan ya kara da cewa, matakai daban daban da gwamnatin Sin ke aiwatarwa domin bunkasa tattalin arziki na ci gaba da ingiza kyautatuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp