A yau Laraba, ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta fitar da alkaluma dake nuna yadda tattalin arzikin masana’antu na kasar ya bunkasa ba tare da tangarda ba cikin rubu’i 3 na farkon shekarar bana. Cikin fannonin dake da nasaba da hakan, bangaren inganta darajar masana’antun kasar ya bunkasa da kaso 5.8 bisa dari cikin shekara guda, inda ya samar da gudummawar kusan kaso 40 bisa dari, ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Kaza lika, jimillar hada hadar kasuwanci mai nasaba da sashen sadarwar tarho, ya karu da kaso 10.7 bisa dari a shekara. Ya zuwa watan Satumba da ya shude, adadin tashoshin samar da hidimar yanar gizo ta 5G da aka kafa a sassan kasar sun kai miliyan 4.089.
Kari kan hakan, sashen ci gaban masana’antun kasar marasa fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, da masu fitar da mafi karancin iskar carbon mai dumama yanayi, sun samu babban ci gaba. A halin yanzu kuma, darajar hajojin da ake samarwa daga masana’antu marasa gurbata muhalli, ta kai kaso sama da 18 bisa dari, cikin jimillar da sashen masana’antun sarrafa hajoji ke samarwa. A daya bangaren kuma, matsakaicin mizanin amfani da nau’o’in makamashi marasa gurbata muhalli, ya haura kaso 50 bisa dari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)