Jiya Juma’a, hukumomi da dama na kasar Sin, sun gabatar da alkaluma daban daban, a fannin tattalin arzikin kasar, na tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, wadanda suka bayyana kwarin gwiwa, da kuzarin bunkasuwar tattalin arzikin kasar ta Sin.
Kididdigar da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar ta nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Agustan bana, yawan jarin kai tsaye da Sin ta zuba a ketare a fannonin da ba na hada-hadar kudi ba, ya karu da kashi 18.8% bisa na makamancin lokaci na bara.
- An Gabatar Da Rahoton Bunkasuwar Kamfanoni Mallakar Gwamntin Tsakiyar Sin Na 2023
- Zargin Daura Aure Da Mai Kanjamau: Yadda Aka Tube Hakimi A Katsina
Ban da wannan kuma, kididdigar da hadaddiyar kungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki ta fitar ta nuna cewa, a cikin wadannan watanni, yawan wutar lantarki da sana’o’in samar da kayayyaki ta amfani da fasahohi masu inganci, da samar da na’urori, ya karu da kashi 9.6%, daga adadin, yawan wutar lantarki, da sha’anin samar da motoci masu amfani da tsabtaccen makamashi, da allunan samar da wutar lantarki ta hasken rana, da sassan na’urori, da sauransu ya karu matuka.
Kaza lika, hadaddiyar kungiyar sufurin kayayyaki da sayayya, sun fitar da kididdigar cewa, yawan kayayyakin da aka yi sufurin su cikin ma’adanar sanyi ya karu da kashi 3.95% a tsawon watannin 8 bisa makamancin lokacin bara. (Amina Xu)