Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara bukatun al’umma, da tabbatar da dorewar samar da aikin yi da daidaiton farashin kaya, da kuma raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, inda aka cimma sabbin nasarori kan neman ci gaba mai inganci.
A fannin masana’antu kuma, yawan kayayyakin da aka samar ya karu da sauri, kana, aikin kera na’urori da aikin samar da kayayyaki da fasahohin zamani suna bunkasuwa kamar yadda ake fatan gani. Har ila yau a watan Yulin, kudin shigar manyan masana’antu ya karu da kaso 5.7 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Haka kuma, kudin shigar masana’antun kera na’urori ya karu da kaso 8.4 bisa dari, kana, karuwar kudin shigar masana’antun sarrafa kayayyaki da fasahohin zamani ya kai kaso 9.3 bisa dari.
Haka zalika, ayyukan ba da hidima suna bunkasuwa da sauri, musamman ma a fannin ba da hidima da fasahohin zamani. Inda yawan kudaden da aka kashe a wannan fanni ke ci gaba da karuwa cikin manyan kasuwanni, kuma harkokin ba da hidima da ba na sari ba, suna bunkasuwa cikin sauri sosai. Kana, yawan jarin da aka zuba kan kadarori ya ci gaba da karuwa, haka ma yawan jarin da aka zuba kan masana’antun kere-kere, wanda yake bunkasuwa cikin sauri. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp