A kwanakin baya, an gabatar da kididdigar tattalin arzikin Sin, da ta shige da ficen kasar Sin, a rubu’in farko na shekarar bana.
Gama da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, tattalin arzikin Sin ya samu farfadowa, wanda hakan ya kara samar da dama ga bunkasuwar sauran kasashen duniya.
Wang Wenbin, ya yi bayani da cewa, a rubu’in farko, yawan kudin shige da fice tsakanin Sin da kasashen kungiyar ASEAN ya karu da kashi 16.1 cikin dari, kana yawansu a tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, ya karu da kashi 14.1 cikin dari, kuma a tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka, ya karu da kashi 11.7 cikin dari.
Kaza lika, yawan adadin a tsakanin Sin da kasashen da shawarar “ziri daya da hanya daya” ke shafa, ya karu da 16.8 cikin dari. Sai na Sin din da kasashen da suka daddale yarjejeniyar RCEP, wanda ya karu da kashi 7.3 cikin dari.
Bisa rahoton hasashen tattalin arzikin duniya, wanda asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya gabatar, an ce, tattalin arzikin Sin na bana, zai samar da gudummawar kashi 1 cikin 3, na jimillar bunkasuwar duniya baki daya. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp