Kasashen Afrika za su iya amfani da huldar dake tsakanin Sin da nahiyar, wajen kawo gagarumin sauyi a tsarin aikin gona, da magance yunwa, da karancin sinadarai masu gina jiki, da kuma habaka tattalin azrikin mazauna karkara, wani babban jami’in asusun bunkasa aikin gona na kasa da kasa IFAD ya bayyana hakan, a yayin tattaunawa ta kafar bidiyo da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Talata.
Guoqi Wu, mataimakin shugaban sashen ayyukan hidima na IFAD, ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Sin ita ce babbar mai samar da gudunmawa ga shirin IFAD cikin kasashe masu tasowa. Ya kara da cewa, Beijing tana kuma yin hadin gwiwa da hukumar musamman ta MDD wajen tabbatar da huldar kasashe masu tasowa da kuma hulda tsakanin bangarori wanda ke amfanar da fannin aikin gona a Afrika.
Ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasar Sin ita ce babbar kasar da ta fi shigo da nau’ikan kayan amfanin gona da suka hada da furanni, da avocados daga kasashen Afrika, al’amarin da ya yi matukar amfanawa manoman karkara.
Wu ya bayyana cewa, kasashen Afrika za su iya koyon darrusa daga kasar Sin, wadda ta yi nasarar kawar da matsanancin talauci da yunwa, bayan da kasar ta yi amfani da wasu manufofi gami da sabbin fasahohi. (Mai Fassarawa: Ahmad Fagam)