An gudanar da kwarya-kwaryar taron shugabanni karo na 31 na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin Asiya da tekun Fasific wato APEC, a birnin Lima na kasar Peru da safiyar ranar 16 ga wata. Wannan shi ne karo na uku da Peru ke karbar bakuncin taron shugabannin kungiyar APEC bayan shekarar 2008 da ta 2016.
A gefen taron, wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, ta samu damar tattaunawa tare da shugabar kasar Peru Dina Boluarte, wadda ta yi nuni cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen mu’amalar tattalin arziki tsakanin mambobi 21 na kungiyar APEC.
- Wasu Kasashe Da Suka Samu Gurbin Zuwa Gasar Cin Kofin Afirka 2025
- Halartar Shugaba Xi Taron APEC Da G20, Da Ziyarar Aiki A Peru Da Brazil Sun Kasance Wata Hanyar Sada Zumunta Da Hadin Gwiwa
A shekarar 1991, kasar Sin ta shiga kungiyar APEC a hukumance. Da take magana game da sauye-sauyen rawar da kasar Sin ta taka, da kuma gudummawar da ta bayar cikin wannan tsarin a shekaru fiye da 30 da suka gabata, Boluarte ta ce, ko shakka babu kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a cikin kungiyar APEC. Ta ce, tashar jiragen ruwan Chancay, wani misali ne na rawar da kasar Sin ke takawa a yankin tekun Fasifik. Shi ya sa Peru ta dade tana yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, wannan shi ma dalilin ne da ya sa Sin ta zama abokiyar cinikayyar Peru mafi girma a halin yanzu.
Ta kara da cewa, Peru za ta ci gaba da karfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, tare da yin koyi da kasar Sin. Peru ta dauki darasi daga kasar Sin a kan yadda za ta fid da kanta daga matsanancin talauci da kuma zama wata kasa mai karfi. Hakan ya koya wa Peru cewa, babu abin da ba zai yiwu ba. (Safiyah Ma)