Da safiyar yau Litinin aka gudanar da bikin tura jami’an ‘yan sanda masu wanzar da zaman lafiya na kasar Sin zuwa Sudan ta Kudu, a sansanin horar da jami’an wanzar da zaman lafiya na ma’aikatar tsaron kasar Sin.
‘Yan sandan na kasar Sin za su tashi zuwa Sudan ta Kudu ne da sanyin lafiyar ranar Laraba, 22 ga wata domin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.
- Daga Yau Litinin Zuwa Laraba Za a Ƙwalla Rana Mai Tsananin Zafi A Wasu Jihohin Nijeriya – NiMet
- Ko Yaushe Ne Palasdinawa Za Su Daina Shan Wahala?
Wani jami’in ofishin kula da hadin gwiwar Sin da kasa da kasa, na ma’aikatar tsaron kasar ya bayyana cewa, a matsayinta na mambar dindindin ta Kwamitin Sulhu na MDD, kuma kasa ta biyu mafi bayar da gudunmuwar jami’an wanzar da zaman lafiya a duniya, kasar Sin na nacewa ga bayar da goyon baya da shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD.
Wannan shi ne karo na farko da Sin za ta tura jami’an ‘yan sandan wanzar da zaman lafiya zuwa Sudan ta Kudu, tun bayan kawar da annobar COVID-19. Haka kuma, ya nuna yadda rundunonin tsaron kasar Sin ke shiga ana damawa da su a shirye-shiryen tsaro na duniya da kuma sauke nauyin dake wuyan kasar Sin a matsayinta na babbar kasa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)