A kwanan baya, mataimakin shugaban kwamitin ba da shawarwari kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin ko CPPCC, Hu Chunhua, ya jagoranci wata tawaga da ta ziyarci Nijeriya, da Cote d’Ivoire da kuma Senegal, inda ya gana da shugabannin majalisar dattijai da ta wakilai na Nijeriya, da firaministan kasar Cote d’Ivoire, da shugaban Senegal da sauran jami’an gwamnati da dama.
Hu Chunhua ya ce, kasar Sin za ta karfafa aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugaba Xi Jinping da shugabannin kasashen uku suka cimma, da kuma sakamakon taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da Afirka a fannoni daban daban, da kuma amfanar da jama’ar bangarorin biyu. Kana kwamitin ba da shawarwari kan harkokin siyasa na jama’ar kasar Sin yana son ba da gudummawa ta wannan fuskar.
Yayin ganawarsu da Hu Chunhua, manyan jami’ai da dama na Nijeriya, da Cote d’Ivoire da kuma Senegal sun jaddada aniyarsu ta bin ka’idar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, tare da bayyana aniyarsu ta yin aiki tare da kasar wajen aiwatar da sakamakon taron kolin Beijing na dandalin tattaunawarta da Afirka, da kara matsa kaimi ga kyautata dangantakar kasashen da Sin, da kuma yaukaka zumuncin Sin da Afirka. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp