Tawagar wasanni ta Babban Birnin Tarayya (FCT), na ci gaba da haskakawa a gasar wasanni ta motsa jiki ta ƙasa karo na 22, wadda ake kira Gateway Games 2024, da ake gudanarwa a Abeokuta, a Jihar Ogun.
A ranar ta biyar da aka ci gaba da fafatawa, tawagar ta FCT ta samu jimillar lambobin yabo 12.
- Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jaridar Da Ya Fallasa ‘Sharrin’ Da Ake Shirya Wa Natasha
- Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram 16 A Borno Bayan Sun Kawo Hari Barikinsu
Wannan ya haɗa da lambobin zinare guda huɗu a wasannin Ayo (2), Golf (1), da Wushu Kung Fu (1).
Sannan kuma sun samu Azurfa guda biyar, huɗu daga ciki an samu su ne a ɓangaren wasannin ɗaukar nauyi, yayin da suka samu tagulla guda uku a wasannin Taekwondo, ƙwallon kafa, da ƙwallon yashi.
Tawagar na fatan ƙara samun lambobin yabo yayin da sauran ake ci gaba da gudanar da wasanni.
A halin yanzu, jihohin da ke saman tebur wajen samun kyauttuka sun haɗa da Legas, Ogun da kuma Birnin Tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp