Tawagar jami’an lafiya Sinawa ta shirya wani horo kan jinyar marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani a wani asibiti dake babban birnin Khartoum na Sudan, a matsayin wata hanya ta musayar fasahohin kiwon lafiya tsakanin kasashe biyu.
Xing Zhijing, daraktan tawaga ta 37 ta jami’an lafiya Sinawa a Sudan, ya ce horon wanda ya gudana a asibitin kawance na Omdurman, ya kunshi lakcoci kan inganta dabarun asibitin na shiryawa kafa cibiyar kula da marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani wato ICU.
Jami’in kula da harkokin kasuwanci na ofishin jakadancin kasar Sin a Sudan, Guo Hu, ya bayyana dadadden tarihin musaya da hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya tsakanin Sin da Sudan, yana mai bayyana hakan a matsayin kyakkyawan misali na abota mai karfi.
A nasa bangaren, Shahd Osman, shugaban sashen kula da dangantaka da kasa da kasa na ofishin kula da harkokin lafiya na kasa da kasa a ma’aikatar lafiya ta Sudan, godiya ya yi matuka ga kokarin Sin na karfafa tsarin kiwon lafiya a kasar. (Fa’iza Mustapha)