Shugaban yankin Zanzibar na kasar Tanzaniya, Hussein Ali Mwinyi ya ba da lambobin yabo da takardun shaidar karramawa ga daukacin mambobin tawaga ta 33 ta jami’an lafiya na Sin, da suka bayar da gudunmawar jinya da kiwon lafiya a Zanzibar.
Kiwon lafiya daya ne daga cikin bangarorin da Sin take hadin gwiwa da kasashen Afrika, inda ta kan tura jami’ai akai-akai domin bada tallafin jinya da horo kyauta. Hadin gwiwar kasar Sin ba abu ne dake mayar da hankali kan moriyarta kadai ba, sabanin yadda wasu suke yada jita jita ko ma suke yi, kasar Sin ta kan taimaka ta kowane bangare da take ganin kasashe masu tasowa, musamman na Afrika na da bukata domin ganin sun samu ci gaba.
- Wang Yi Da Jake Sullivan Sun Gudanar Da Sabon Zagaye Na Muhimmin Tattaunawa Tsakanin Sin Da Amurka
- Inganta Raya Shawarar BRI Zai Zama Daya Daga Manyan Batutuwan Da Za A Tattauna A Gun Taron Kolin FOCAC Na Bana
Tun daga shekarar 1963, kasar Sin ta fara tura jami’an kiwon lafiya kasashen duniya. Cikin shekaru 60 da suka gabata, ta tura jami’an da yawansu ya kai 30,000 zuwa kasashe da yankunan duniya 76, tare da jinyar mutane miliyan 290. Kuma yayin da wadannan jami’an lafiya ke zuwa kasashen, su kan tafi da magunguna da kayayyakin jinya da gwaje-gwaje da sauransu, domin tabbatar sun bada ingantaccen kiwon lafiya.
A kwanakin baya, na hadu da wata kwararriyar likitar ido ta kasar Sin mai suna Dr. Li Yun. Tun daga shekarar 2016, Li Yun ta je nahiyar Afrika sau 4, inda ta gudanar da tiyatar ido fiye da 500. Kuma duk da cewa ta dawo kasar Sin, har yanzu ba ta yanke hulda da kasashen da ta je, har yanzu ta kan tattauna da su ko gudanar da taron karawa juna sani kan abubuwan da suka shige musu duhu.
Yanzu haka akwai tawagogin lafiya na Sin dake aiki a wurare 115 dake kasashe 56 na fadin duniya, kuma galinbinsu wurare ne masu nisa da koma baya. Duba da irin ci gaban kasar Sin da kyautatuwar yanayin rayuwa, wadannan jami’ai sun cancanci yabo matuka, domin sun sadaukar da kansu da jin dadinsu wajen ganin sun taimakawa burin kasarsu na ganin ta taimakawa masu bukata. A kullum na kan ce, daya daga cikin tubalin ci gaban kasar Sin shi ne, yadda al’ummarta ke da kishi da kaunar kasarsu da kuma kyakkyawar fahimta da hadin gwiwa dake akwai tsakanin gwamnati da al’umma. (Fa’iza Mustapha)