Bisa gayyatar bangaren Rwanda, shugaban sashen kasa da kasa na kwamitin kolin JKS Liu Jianchao, ya jagoranci tawagar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) don halartar bikin rantsar da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame a ranar Lahadi da Litinin a birnin Kigali.
A yayin ziyarar, Liu ya yi musayar ra’ayi da shugaba Kagame tare da ganawa da babban sakataren jam’iyyar Patriotic Front Wellars Gasamagera. Liu ya tattauna dangantakar dake tsakanin Sin da Rwanda da bangaren kasar Rwanda, tare da tallata ka’idojin jagoranci na cikakken zaman taro na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20.
Bangarorin biyu sun amince tare da aiwatar da muhimman matsaya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa mu’amala tsakanin jam’iyyun, da kara yin shawarwari a siyasance, da karfafa amincewar juna bisa manyan tsare-tsare, da zurfafa hadin gwiwa a karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. (Mohammed Yahaya)