Tawagar likitocin kasar Sin ta 26 dake aiki a kasar Saliyo, ta gudanar da tiyatar dashen yatsa irinta ta farko da aka kammala cikin nasara a kasar dake shiyyar yammacin Afirka.
An gudanar da aikin tiyatar ne ranar Juma’ar da ta shude, bayan da yatsan hannu na wani mai aikin lantarki mai suna Sallieu Sorious Yusifu Conteh ya tsinke, lokacin da yake aiki a wani wurin hakar ma’adanai dake gundumar Port Loko ta lardin arewa maso yammacin kasar.
Kafofin watsa labaran kasar sun jinjinawa kwarewar tawagar likitocin ta Sin, suna masu bayyana nasarar tiyatar da matakin da ka iya zurfafa hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya tsakanin Sin da Saliyo. (Mai fassara: Saminu Alhassan)