Hukumar kula da harkokin sararin samaniya ta kasar Sin ta ce, yayin babban taron kasa da kasa kan harkokin sararin samaniya karo na 74, tawagar ma’aikatan na’urar binciken duniyar wata mai suna Chang’e 5 ta kasar Sin, ta samu lambar yabo da ake kira “Laurels for Team Achievement”, wadda ta kasance lambar yabo mafi girma da cibiyar nazarin harkokin sararin samaniya ta duniya wato IAA a takaice ta kan bayar ga wata tawaga. A wajen taron kuma, hukumar kula da harkokin sararin samaniyar kasar Sin ta sanar da cewa, kasa da kasa za su iya neman izini daga wajenta don gudanar da bincike kan samfuran duniyar wata da na’urar Chang’e 5 ta kawo.
Aikin na’urar Chang’e 5, shi ne na farko da kasar Sin ta gudanar wajen tura wata na’ura ba tare da dan Adam ba zuwa duniyar wata, don dauko samfura daga can, wanda ya kasance babban aiki dake kunshe da fasahohin zamani masu tarin yawa a fannin nazarin sararin samaniya. Bayan doguwar tafiya, na’urar Chang’e 5 ta dauko samfuran da nauyinsu ya wuce kilogiram 1.7 daga duniyar wata, wanda ya zama samfuran duniyar wata mafi yawa da aka dauko lokaci guda, ba tare da dan Adam ba a duniya.
An kafa lambar yabo ta “Laurels for Team Achievement” a shekara ta 2001, wadda daya ce daga cikin manyan lambobin yabo guda biyu da cibiyar IAA ta kan bayar a kowace shekara, da zummar jinjinawa tawagogin da suka yi fice a bangaren nazarin harkokin sararin samaniya, musamman a fannonin da suka shafi kirkire-kirkiren fasahohi, gano sabbin abubuwa, da inganta hadin-gwiwar kasa da kasa. (Murtala Zhang)