Tawagar Sin ta dindindin a hukumar samar da abinci da raya aikin gona ta MDD (FAO) ta fara aiki a hukumance a jiya Alhamis.
A watan Afrilu na shekara ta 1973, Jamhuriyar Jama’ar Sin ta dawo da halaltaccen matsayinta a hukumar FAO, kuma a shekara ta 1982 ta kafa ofishin wakilinta na dindindin a hukumar. A shekara ta 2020, aka daga matsayin ofishin zuwa na jakadanci. Daga baya kuma, a watan Agusta na shekara ta 2025, aka daga matsayin ofishin zuwa na tawagar dindindin a hukumance.(Amina Xu)