A yau Lahadi, tawagar ‘yan sama jannati na kumbon Shenzhou 19 na kasar Sin suka gudanar da bikin mika ragamar ayyuka ga tawaga ta 20, tare da mika musu mukulan tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin.
Yanzu, tawagar ‘yan sama jannati na Shenzhou 19 ta riga ta kammala ayyukanta da aka tsara. ‘Yan sama jannatin 3 za su dawo ne cikin kumbon Shenzhou 19, inda za su sauka a wurin saukar kumbuna na Dongfeng dake jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta a yankin arewacin kasar Sin, a ranar 29 ga wata.
Yanzu haka, an kammala shirya dukkan ayyuka da ma wajen saukar kumbon domin maraba da mutanen 3. (Fa’iza Mustapha)