A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)