Labarin Tesla a kasar Sin ya kasance wani abin nazari kan yadda kasar ke bude kofarta, da yanayin kasuwanci da karfin masana’antu a bangaren motocin sabbin makamashi (NEV), kana ya bayyana damar yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Bara mu fara da Gigafactory na Tesla dake Shanghai wanda shi ne kamfanin kera motocin sabbin makamashi mallakin wata kasa daga waje a kasar Sin. An gina kamfanin tare da kaddamar da shi a cikin shekara guda a shekarar 2019. Yanzu shi ne ke dauke da fiye da rabin kayayyakin da Tesla ke samarwa a duniya. Megafactory kuwa, wato kamfanin Tesla na biyu a Shanghai, an kammala shi kimanin watanni bakwai bayan da aka fara aikin gina shi a watan Mayun 2024. Saurin ban mamaki na wadannan ayyukan biyu na nuni da kyawawan manufofi da yanayin kasuwa da kasuwancin kasar Sin. Bugu da kari, an saka Tesla a cikin jerin sunayen kamfanoni masu saye da sayarwa na kananan hukumomi da dama, wanda ke nuna yadda kasar Sin ke daidaita harkokin kasuwancin cikin gida da na waje.
Babu shakka, jarin Tesla a kasar Sin nasara ce kuma ya samar da kyawawan sakamako na samun moriyar juna. Wannan ba abu ne mai yiwuwa ba tare da tsayin daka wajen tabbatar da bude kofa ga kasashen waje ba, da kokarin da take yi na inganta yanayin kasuwancinta. Hakazalika, tambarin Tesla sanannen alama ce a tsakanin masu amfani da abeben hawa Sinawa, saboda kimanin kashi biyu bisa uku na motocin da kamfanin na Gigafactory na Shanghai ya kera a kasar Sin ake sayar da su, yayin da ake fitar da ragowar kashi dayan zuwa kasuwannin ketare kamar kasashen Turai. Sakamakon bukatu mai karfi na cikin gida a yayin yunkurin kasar na sauyi zuwa amfani da ababen hawa mara gurbata muhalli, masana’antar NEV ta kasar Sin ta samu babban ci gaba a ‘yan shekarun nan. A shekarar 2024 alal misali, abin da aka fitar na NEV na kasar Sin ya zarce guda miliyan 10 a karon farko, kuma Tesla yana daya daga cikin manyan masu ba da gudummawa ga wannan adadi. (Mohammed Yahaya)