• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

by Leadership Hausa
3 hours ago
Thomas

‘Yan kasuwar Nijeriya kaɗan ne da za su ɗaukar ma ransu, iya tsayawa da ƙafafunsu da kuma gina ƙasa kamar yadda Thomas Etuh, Shugaban Kamfanin Mikap Group masu yin takin zamani da sauran kayan noma ga manoman Nijeriya (FEPSAN).

Kamar yadda ya fara daga  tsakiyar Arewacin Nijeriya zuwa ɗaya daga cikin masu harkar kasuwanci na lamarin aikin noma, Etuh ya nuna cewa kamfanoni masu zaman kansu —da suke taimaka wa wasu suma domin  su kai ga cimma burinsu, domin kuwa maganar gaskiya akwai samun nasarar ciyar da mutane, su kuma kasance cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya—.

Ƙarƙashin kulawarsa takin zamani ya daina zama wani abin da kafin a same shi sai an sha wahala, ko kuma a yi amfani da siyasa, amma ya zauna ya yi wani abin da ake tallafa wa milyoyin al’umma ƙananan manoma a faɗin tarayyar Nijeriya.

“Aikin noma ba wai kawai kasuwanci ba ne kaɗai kamar yadda ya ce,”. “Aikin gona babban Tubali ne na tsaron ƙasa.”

Ciyar da ƙasa da gyara a lokaci ɗaya

LABARAI MASU NASABA

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

Lokacin da Etuh ya zama wanda ake maganarsa  musamman ma idan an taɓo maganar Takin zamani,  masana’antar ta kama hanyar lalacewa saboda ‘yan baran da sun mamaye ta, ga kuma cuwa-cuwa da ta yi wa wurin katutu, lamarin da ke sa ba a iya gane manoman gaskiya.

Duk da hakan ba ta sa Etuh ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen haɗa kan da ya yi da gwamnatin tarayya, Etuh ya taimaka wa tsarawa da kuma gabatar da lamarin Takin zamani na Shugaban ƙasa Bola Tinubu (PFI),lamarin da ya kawo gaggarumin ci gaban aikin gona, domin kuwa an samu raguwar farashi,ya kuma samar da wata kafa inda manoma suke samun Takin zamanin kai tsaye.

Thomas

Sakamakon haka ya sa yanzu an ƙara samun ci gaba, domin da farko ana da inji  1 ake amfani da shi a shekarar 2016, Nijeriya  yanzu tana da injuna fiye da 70 duk kuma mashin ɗaya yanzu akwai hanyar samar da ayyuka , yin takin,  da kuma bunƙasa ƙauyuka.

Kamfanin Etuh’s Mikap tare da tawagar FEPSAN  sun haɗa kansu wajen samar da Takin zamani fiye da buhuna miliyan 50  na takin zamani mai suna Kamfa ko kuma NPK  a ƙasa baki ɗaya, hakan ya sa an bar dogara da shigo da shi Takin daga ƙasashen waje, an kuma ceto Nijeriya daga amfani da biliyoyin Naira ta hanyar kuɗaɗen ƙasashen waje.

Taimakawa wajen yin takin zamani na gida

Hangen nesa irin na Etuh abin ya wuce maganar Takin zamani. Saboda yana son bunƙasa aikin noman ne daga ciki zuwa waje— daga lokacin shukawa zuwa har ya kai ga nuna a yi girbi a kawo gida ko kuma zuma kasuwa.

Ta hanyar Kamfanin Mikap Nijeriya, ya zuba jari na yadda ake yin Takin zamani da inji,  yadda za a kai shi gida bayan an girbe,  kai shi wurin ajiya, tabbatar da cewa an bar noma ta  kai ga shigar kowane ɓangare na tattalin  arziki.

Ganin yadda ya maida hankali ya sa gwamnatocin Jihohi suka haɗa kai da shi, ƙungiyoyin tsimi da tanaji, da kuma  ƙananan Bankuna da suke harkar kuɗaɗe, suna ba da dama ta bayar da bashi ga ƙananan manoma waɗanda suka rasa waɗanda za su ba su bashi.

A kowace Jiha inda ake yin wannan tsarin, rayuwar jama’a ta inganta, matasa sun samu aikin yi, yayin da mata kuma suka samu madafar da za su tsaya da ƙafafaunsu.

Yadda ake amfana da Thomas Etuh

An raba buhunan Takin Zamani miliyan 50 a faɗin tarayyar Nijeriya

An gyara injinan yin Taki fiye da Injina 70 da kuma sake  duba wasu, inda dubban manoma suka amfana da irin taimakon kai tsaye.

An samu dubban ayyukan yi sanadiyar lamarin na Takin Zamani.

An hana kashe bilyoyin kuɗaɗen ƙasar wajen da za a yi amfani da su saboda shigo da Takin da ake yi cikin gida Nijeriya wanda ake yi ta hanyar amfani da kayan gida.

Kowane ya samu wakilci ba kawai ya cancanci abin da ya samu ba, sai dai kuma babban jin daɗi— an samu ƙaruwar jin daɗin ‘yan Nijeriya.

Daga tsarin Takin  Zamani na Gida Zuwa Ga Tsari Ko Manufar Nijeriya

A matsayin shi na Shugaban masu yin Takin Zamani da raba shi na ƙasa (FEPSAN), Etuh shi ya kasance murya wanda ya damu da yadda ɓangaren yake.

Ya jagoranci maganar samar da kayan da za a haɗa wajen yin Takin Zamani, domin tabbatar da cewar masana’antun kamar su limestone, urea, da phosphate sun zama sune abubuwan da za ‘a riƙa yin amfani da su wajen yin shi Takin Zamanin.

Haka nan ma shi ne jagora na kula da ingancin shi Takin Zamanin yin hakan kuma an samu maganin waɗanda suke shigo da Takin Zamani da baya da inganci. Manoma yanzu suna samun Takin Zamani wanda ya dace da yanayin da ƙasar gonarsu take da kuma irin amfanin gonar  da za su shuka— domin kimiyya ta sa an bar yin cece- kuce ana amfani da zarihi ne.

Ta hanyar tattaunawar da yake yi da masu aiwatar da tsare tsare, Etuh ya taimaka wajen kawo gyara kan lamarin daya shafi Takin Zamani na ƙasa yadda za a inganta shi, wanda yanzu ɗauki matakin ya sa ana amfani da irin matakin da aka yi amfani da shi a nahiyar Afirka ta kudu da Sahara.

Abin ya wuce kasuwanci har da taimaka wa al’umma

Yadda Etuh yake manufa da sha’awa ta taimakawa al’umma domin su samu ci gaba. Ta hanyar gidauniyar Thomas Etuh, ya taimaka wa ɓangaren ilimi, lafiya, da kuma tallafa wa matasa a Jihohin  Kogi, Benuwe, da kuma Nasarawa.

Ya ba da tallafin ga ɗalibai ‘yan asalin Jihar, da kuma ba su horo ta ɓangaren aikin gona, da kuma ba da tallafi domin ƙananan masana’antu inda za a riƙa sarrafa abin da aka noma saboda ƙungiyoyin mata.

A shekarar 2024, gidauniyar ta ƙaddamar da tsarin Green Rural Initiatiɓe, wanda  ke da sabbin manoma — 5,000  kowace shekara. Tsarin yana nuna duk ƙaryar ci gaban Birane da ƙauyuka suke taƙama.

Shugaba mai niyyar taimako

Ya san yadda zai ja hankalin mutane ta hanyar iya maganarsa, an  san Etuh kan yadda yake shirye- shiryen shi ,  ga shi da son taimakon al’umma da kuma haɗin kai.

Abokan harkokinsa sun shi mutum ne wanda Allah ya sa ma shi tausayi na taimakawa, sai dai kuma duk wani , matakin da zai ɗauka sai ya yi tunani tukuna—ɗa bi;un nasa su sukka sa al’umma suka amince da shi har ma tare da gwamnati.

Ya yi karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, ya kuma samu horo kan tsare-tsare da manufofi na manyan jami’ai a nan cikin gida da kuma waje, Etuh ya kawo ƙwararru ƙwarai da gaske zuwa ga ɓangaren waɗanda wani lokaci ba a ɗaukesu da muhimmanci ba. Manyan jami’an da yake yi aiki da su sun kwashe shekaru masu yawa a masana’antu, harkar kuɗaɗe da kuma ci gaba, amma duk da hakan babban abin da ya fi damuwa da sa shi ne ƙasar da ake yin noman a kanta, saboda ita ce babbar ma’aikatar dukiya.

Yadda ya samu jinjina daga gida da waje

A ƙarƙashin jagorancin Etuh, masana’antar takin zamani ta Nijeriya ta samu gagarumin nasara a nahiyar. Ƙungiyoyin yankin kamar irinsu Ƙungiyar Haɗin Gwiwar Takin Zamani da Kasuwancin Noma na Afirka (AFAP) da Shirin Haɓaka Noma a Afirka (AGRA) sun amince da haɗin gwiwa da Nijeriya a harkar noma da kamfanoni masu zaman kansu suka jagoranta.

Ya sama lambobin yabo masu tarin yawa a harkokin kasuwanci da samar da kayayyaki na ƙasa da ƙasa da kuma ɓangaren shugabancin noma, amma Etuh babbar bajintarsa ta fi shahara lokacin girɓin amfanin gona.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu
Manyan Labarai

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin
Manyan Labarai

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Next Post
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

LABARAI MASU NASABA

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

Fiye da Janarori 50 Za Su Yi Ritaya Bayan Sabbin Naɗe-Naɗen Tinubu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi

October 25, 2025
Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.