A yau Lahadi ne mataimakiyar shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Tie Ning, ta halarci bikin bude taron karawa juna sani na ‘yan majalisun dokokin kasashen Afirka, wanda majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta dauki nauyin shiryawa a birnin Beijing.
Cikin jawabin da ta gabatar yayin kaddamar da taron, Tie ta ce, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a taron koli na mata na kasa da kasa wanda ya gudana a kwanan baya, mai kunshe da shawarwarin Sin ga ingiza sabuwar tafiyar bunkasa ci gaban mata a dukkanin fannoni, ya samu matukar karbuwa daga sassan kasa da kasa.
Tie Ning ta kara da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin mahalarta, wajen aiwatar da sakamakon taron kolin na mata, da taro Beijing na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ko FOCAC, ta mahangar majalissun kafa dokoki, da kyautata musaya ta abokantaka tsakaninsu, da karfafa musayar kwarewa ta fuskar jagoranci, da bunkasa kariyar da doka ke baiwa hakkoki da moriyar mata, da hada karfi wajen gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama. (Saminu Alhassan)